Mali-ECOWAS

Tawagar ECOWAS sun ce sun kammala aiki a Mali

Tawagar ECOWAS a Mali da Guinea Bissau dake fama da rikicin Siyasa
Tawagar ECOWAS a Mali da Guinea Bissau dake fama da rikicin Siyasa AFP PHOTO/ SIA KAMBOU

Tawagar masu sa Ido ta kungiyar ECOWAS a kasar Mali sun ce sun cim ma bukatunsu bayan amincewa da wanda zai jagoranci gwamnatin wuccin gadi tare da ba Kaftin Sanogo mukamin Tsohon shugaban kasa.

Talla

Bayan kwashe kwanaki Wakilan ECOWAS suna tattaunawa da Gwamnatin Soji, bangarorin biyu sun amince Kaftin Sanogo ya mika mulki tare da samun kariyar Tsohon shugaban kasa.

A ranar 22 ga watan Maris ne Sojoji suka kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure karkashin jagorancin Kaftin Amadou Sanogo.

Sojojin sun ce sun karbe iko ne saboda gazawar Gwamnati wajen yaki da ‘Yan Tawaye wadanda suka karbe ikon Yankin Arewaci.

Masu lura da al’amurra a kasar Mali suna ganin rikicin ‘Yan Tawaye shi zai kawo cikas ga kokarin kafa gwamnatin wuccin gadi a kasar.

Karkashin yarjejeniyar, Gwamnatin Wuccin gadi zata kwashe watanni 12 tana shugabanci, kuma Dioncounda Traore, shi ne zai kasance shugaban kasa har zuwa gudanar da zabe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.