Libya-Tunisia

Baghdadi ya shiga yajin cin Abinci don gudun kada a mayar da shi Libya

Tsohon Fira Ministan Libya Al-Mahmoudi
Tsohon Fira Ministan Libya Al-Mahmoudi AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA

Tsohon Fira Ministan kasar Libya Baghdadi al-Mahmoudi da ke kasar Tunisia, ya fara yajin cin abinci, don kaucewa yiwuwar mayar da shi kasar shi, don yanke ma shi hukunci. Kamar yadda lauyan shi ya tabbatar.

Talla

Lauyan Mahmoudi Mabrouk Kourchid yace tsohon Fira Ministan ya fara yajin ne a ranar Assabar ne bayan da Fira Ministan Tunisia Hamadi Jebali ya ce kasar shi ba za ta kasance mafaka ga wadan suka yi barazana ga zaman lafiya Libya ba.

Mahmoudi, da ake tsare da shi tun cikin watan Satumban bara, na daya daga cikin mutanen da hukumomin birnin Tripoli ke ta ganin an mika masu shi, kuma gwamnatin Tunisia ta yi alkawarin cika wannan burin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.