Masar

Gwamnatin Sojin Masar ta yi kiran amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa

'Yan takarar Shugaban kasar Masar : Mohamed Selim al-Awa, Mahmoud Hossam, Abdullah al-Ashaal, Mohamed Fawzi Eissa, Hisham al-Bastawisy da  Ahmed Shafik .
'Yan takarar Shugaban kasar Masar : Mohamed Selim al-Awa, Mahmoud Hossam, Abdullah al-Ashaal, Mohamed Fawzi Eissa, Hisham al-Bastawisy da Ahmed Shafik . REUTERS

Gwamnatin Mulkin Sojin kasar Masar ta yi kira ga ‘Yan kasar su amince da samakon zaben shugaban kasar karo na farko da za’a gudanar tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak a farkon shekara da ta gabata.

Talla

Majalisar Mulkin sojin tace sakamakon zaben zai nuna abin da ‘Yan kasa ke bukata.

A ranar laraba mai zuwa ‘Yan kasar su kusan miliyon 50 ne za su zabi wanda zai jagoranci kasar, tsakanin ‘Yan takarar da suka hada da Amr Mussa, Ahmed Shafiq, Mohammed Mursi da Abdel Moneim Abul Fotouh.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.