Mali

Masu zanga-zanga sun raunata shugaban rikon Mali

Masu zanga-zangar neman Dioncounda Traore ya yi murabus a Mali
Masu zanga-zangar neman Dioncounda Traore ya yi murabus a Mali AFP/HABIBOU KOUYATE

An kwantar da Dioncounda Traore Asibiti, shugaban rikon kwarya a kasar Mali, bayan wani hari da masu zanga-zanga suka kai a fadar shugaban kasa wadanda suka nemi ya yi murabus. Rahotanni daga Mali na cewa an fasa ma shi Kai.

Talla

Kakakin sojin kasar da suka hambarar da gwamnatin Toumani Touri yace Jami’an tsaro sun kashe mutane uku cikin masu zanga zangar a fadar shugaban kasa.

Kasar Mali dai yanzu ta shiga wani hali na rikicin Siyasa da rikicin ‘Yan Tawayen Azbinawa da suka karbe ikon Arewaci. A karshen mako ne Kaftin Sanogo jagoran juyin Mulkin kasar ya amince Troure ya ci gaba da jagorancin Rikon kwarya al’amarin da ya fusata wasu ‘yan siyasar Mali.

Rikicin siyasar kasar Mali wani kalubale ne ga kasashen Yammaci wadanda ke kokarin taimakawa kasar wajen yaki da ‘Yan Tawaye.

Rahotanni dai na cewa  masu Zanga-Zanga sun yi wa Traore duka tare da yin kaca-kaca da tufafin shi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.