Zambia

Kotu a Zambiya ta daure wani tsohon minista na zaman gidan yarion shekaru 2

Золотов/Wikipedia

Wata Kotu a kasar Zambia ta daure wani tsohon Ministan kasar , Austin Liato, saboda samun sa da boye miliyoyin kudaden kasar a gonarsa. 

Talla

Austin Liato wanda ya rike Ma,aikatar Kwadago ta kasar , tun watan 12 na shekarar data gabata aka kama shi, bayan gano rumbunan da ya gina har biyu, a karkashin kasa, da kuma ya  shake su da kudaden kasar, da ake kira Kwacha, da suka zarta biliyan 2.

Alkalin kotun ya daure tsohon Ministan na tsawon shekaru biyu da aiki mai tsanani.

Wannan shine karo na farko da Gwamnatin Shugaba Micheal Sata ta hukunta wani jamiin saboda irin wannan laifi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.