Masar

Brotherhood ta yi ikirarin samun nasara a zaben Masar

Wata Tutar Muhamed Moursi a Ginin Hedikwatar Jam'iyyar Botherhood a Birnin al Kahira.
Wata Tutar Muhamed Moursi a Ginin Hedikwatar Jam'iyyar Botherhood a Birnin al Kahira. Daniel Finnan

Jam’iyyar Brotherhood ta 'Yan uwa Musulmi a kasar Masar, ta bayyana samun gagarumar nasara a kidayar kuri’un zaben shugaban kasa, bayan kidaya rabin kuri’un mazabun kasar. Jam’iyar tace, Dan takaranta Mohammed Mursi ne akan gaba da kashi sama da 30, sai kuma Ahmed Shafiq a matsayi na biyu da sama da kashi 22.

Talla

Hamdeen Sabbani ne a matsayi na Uku da kashi 20 karkashin sakamakon da Jam’iyyar Brotherhood ta bayar a mazabu 6,661 cikin mazabu 13,000.

‘Yan takara 12 ne dai suka shiga zaben shugaban kasa inda Al’ummar Masar Miliyan 50 ka da yancin kada kuri’a.

An dai gudanar da zaben ne cikin kwanciyar hankali da Lumana ba tare da wani rikici ba.

Wannan kuma zabe ne mai dimbin tarihi a kasar Masar domin shi ne zaben Farko bayan kwashe watanni ana gudanar da zanga-zangar da ta yi awon gaba da Hosni Mubarak wanda ya kwashe tsawon shekaru 30 yana shugabancin Masar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.