Zimbabwe-Bankin Duniya-Najeriya

Mugabe ya soki kasashen Duniya game da shugabancin Bankin Duniya

Jim Yon Kim, wanda aka zaba sabon shugaban Babban Bankin Duniya wanda ya kada Ngozi Okonjo-Iweala,  Ministan kudin Tarayyar Najeriya
Jim Yon Kim, wanda aka zaba sabon shugaban Babban Bankin Duniya wanda ya kada Ngozi Okonjo-Iweala, Ministan kudin Tarayyar Najeriya REUTERS/Issei Kato/Nicky Loh - Montage RFI

Shugaban Kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya yi mummunar suka kan matsayin da kasashen yammacin duniya suka dauka, wajen hana Ministan kudin Najeriya, Ngozi Okonjo Iweala mukamin shugaban Bankin Duniya.

Talla

Mugabe yace Afrika ta yi bakin-cikin rashin samun Mukamin shugabancin Babban bankin a lokacin da ya ke shaidawa wani taron mata a Harare, wanda Ngozi Okonjo Iweala ke halarta.

Shugaban yace, babu Dan Afrika da zai shugabanci Bankin Duniya da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya, abinda ke dada nuna rashin daidaito a tsakanin kasashen duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.