Najeriya

Najeriya na hasarar gangan Mai 180,000 a rana, inji NNPC

Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya
Ginin Kamfanin NNPC a Najeriya RFI

Kamfanin NNPC a Najeriya yace ana hasarar gangan Mai 180,000 da ake sacewa a rana. Shugaban Hukumar Austen Oniwon ya nemi taimakon Majalisa domin gaggauta fito da hanyoyin magance matsalar.

Talla

Mista Oniwon yace adadin Man da ake sacewa a rana ya fi karfin adadin wanda kasar Ghana ke fitarwa a rana.

Kasar Ghana tana fitar da gangan mai 120,000 ne a rana inji Oniwon.

Najeriya dai tana cikin manyan kasashe Takwas masu fitar da Mai a Duniya, kuma kasa mai yawan mutane a Afrika, amma Ghana ba da dadewa ba ne ta fara hako Manta, kuma Ghana tana da yawan Mutane Miliyan 24 sabanin Najeirya mai yawan mutane Miliyan 169.

A watan Mayu ne shugaban Kamfanin Shell mai kula da tashar Najeriya Mutiu Sunmonu, ya bayyana cewa Najeriya tana hasarar Kudi Dala Biliyan Biyar ($5b) duk shekara.

A farkon shekarar 2012 ne Gwamnatin Jonathan ta janye tallafin Mai wanda ya haifar karin farashin Man daga N65 zuwa N145 kafin adawo da farashin N97 bayan barkewar zanga-zanga daga sassan yankunan Najeriya.

Gwamnatin Jonathan tace janye Tallafin ita ce hanya guda da za’a samar da ci gaba mai daurewa a Najeriya.

Sai dai Al’ummar Najeriya suna ganin tallafin Man Fetir shi ne abu guda da suke more arzikin da Allah ya albarkaci kasar da shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.