Mali

Shugaban rikon Mali yana Faransa wajen jinya

Shugaban rikon gwamnatin Mali, Dioncounda Traoré
Shugaban rikon gwamnatin Mali, Dioncounda Traoré AFP PHOTO / SEYLLOU

Shugaban rikon kwaryar kasar Mali, Dioncounda Traore, ya isa kasar Faransa don kula da lafiyar shi sakamakon harin da masu zanga zanga suka kai a Bamako fadar Shugaban kasa domin neman shugaban ya yi murabus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa, Bernard Valero, yace shugaban zai dauki kwanaki a kasar don samun magani.

Talla

Fira Ministan kasar, Modibbo Diarra, ya shaidawa al’ummar ta gidan talabijin cewa, shugaban ya fara murmuje wa.

A ranar Laraba ne aka kwashi Traore zuwa birnin Paris domin duba lafiyar shi sakamakon raunin da masu zanga-zangar neman ya yi murabus suka yi ma shi.

Kasashen Faransa da Amurka sun yi tir da al’amarin wanda suka danganta a matsayin karan-tsaye ga Demokradiya.

A ranar litinin ne aka kai wa Traore hari bayan Sojojin kasar sun Amince Traore ya jagoranci Mali tsawon shekara domin jagorantar gudanar da zabe, karkashin jagorancin kungiyar ECOWA.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.