Sudan-Sudan ta Kudu

Al Bashir yace zai janye dakarun Sudan daga Abyei, inji Carter

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir a lokacin da zai gabatar da jawabi a gaban ma'aikatan hako mai a Khartoum.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir a lokacin da zai gabatar da jawabi a gaban ma'aikatan hako mai a Khartoum. REUTERS/Stringer

Tsohon Shugaban kasar Amurka, Jimmy Carter, yace Omar Hassana al Bashir ya shaida masa a shirye ya ke ya janye dakarun Sudan daga Yankin Abyei da ake takaddama tsakanin Sudan da Sudan ta kudu. Carter yace wannan ci gaba ne a kokarin sasanta bangarorin biyu.

Talla

Akwai dai yiyuwar barkewar yaki tsakanin Sudan da Sudan ta kudu game da rikicin iyakokin kasashen biyu masu arzikin man Fetir.

Bayan ganawa da Al Bashir, Mista Carter ya shaidawa manema labarai cewa Al Bashir ya amsa zai janye dakarun Sudan daga yankin Abyei da ake takaddama akai.

A watan Mayu ne Sudan ta karbe ikon yankin Abyei wanda yasa daruruwan mutane a yankin yin gudun hijira bayan wasu hare hare da Sudan ta kudu ta kaddamar akan dakarun Sudan.

A ranar 17 ga watan Mayu ne Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Sudan janye dakarunta daga yankin Abyei, amma Sudan ta bijere wa kudirin.

Ana sa ran Sudan da Sudan ta Kudu zasu sake zama a teburin sasantawa a ranar 29 ga watan Mayu a birnin Addis Ababa tare da masu shiga tsakani na kungiyar Tarayyar Afrika.

Kimanin mutane Miliyan Biyu ne suka mutu sanadiyar yakin basasa a shekarun baya a Sudan kafin ballewar yankin Kudanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.