Rwanda-Congo

kasar Rwanda ta yi watsi da wani rahoton sirri na Majalisar dinkin duniya da ya zarge ta

Kasar Ruwanda ta yi watsi da wani rahoton sirri na majalisar dinkin duniya da ke cewa, kasar na dauka tare da horar da mayaka domin taimakawa tsohin yan tawayen kasar Jamhuriyar demokradiyar Congo, wadanda ke fada da gwamnatin kasar ta Congo, tun farkon wannan wata na mayu a yankin arewacin Kivu dake gabashin kasar.A cikin wata sanarwa a yau litanin, ministan harakokin wajen kasar ta Ruwanda Louise Mushikiwabo, ya bayyana cewa, wannan zargi shaci fadi ne kawai, babu kanshin gaskiya a cikinsa