Najeriya

‘Yan Bindiga sun bude wuta a gidan Wani Malamin Shi’a a Potiskum

Wani Harin Bom da aka kai Kaduna
Wani Harin Bom da aka kai Kaduna Reuters / Stringer

Wasu ‘Yan Bindiga sun bude wuta a gidan Wani Malamin Shi'a a Birnin Potiskum, inda suka kashe mutum daya tare da raunata wasu da dama.Shedun gani da ido yace a gidan Wani Limanin wakilin ‘Yan Brother ne mai suna Mustapha ‘Yan Bindigan suka bude wuta kusa da Masallacin da malamin ke bayar da Sallah.

Talla

Bayanai daga Potiskum sun ce Malam Mustapha yana cikin Malaman da suka kalubalanci Jami’an tsaro akan hare haren da aka kai a kwanan baya a wata Kasuwar shanu da aka samu mutuwar mutane 34. Kuma yana cikin Malaman da ke wa’azin kalubalantar Kungiyar Boko Haram.

Kanal Dahiru Abdussalam ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa wasu ‘Yan bindiga ne da ba’a tantance ba suka kai hari a masallacin mabiya shi’a.

Wani shedun gani da ido ya shaidawa Rediyo Faransa cewa direban Malam Mustapha ne aka kashe amma Malamin Allah ya kubutar shi. Sai dai mutane Hudu ne suka samu rauni.

Yanzu haka dai an girke Jami’an tsaro a yankin da aka kai harin tare da kaddamar da binciken wadanda suka kai harin.

Shedun gani da ido yace an kwashe tsawon minti Talatin ana harbe harbe bayan kammala Sallar Magariba a jiya Lahadi.

Sai dai Shedun yace an harbe mutane 4 ‘Yan uwan Malamin.

Jami’an kiyon lafiya a birnin Potiskum sun tabbatar da samun mutuwar mutane Biyu cikin mutane Biyar da aka kawo Asibiti da aka harba da harsashe.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.