Masar

‘Yan Salafi zasu goyi bayan Brotherhood a zaben Masar zagaye na biyu

Gangamin magoya bayan muhammed Mursi dan takarar shugabancin kasa karkashin tutar Jam'iyyar Brotherhood
Gangamin magoya bayan muhammed Mursi dan takarar shugabancin kasa karkashin tutar Jam'iyyar Brotherhood REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Jam’iyyar ‘Yan Salafi ta Al Anur tace zata goyi bayan Mohammed Mursi dan takarar Jam’iyyar Brotherhood a zaben Masar zagaye na biyu don kayar da tsohon Fira minista Ahmed Shafiq.

Talla

“ Jam’iyyar Al Nur zata bada goyon bayanta ga Dakta Muhammed Mursi domin samun nasarar lashe zaben shugaban kasa” kamar yadda jam’iyar ta yada a shafin Intanet na Twitter.

Har yanzu ana dakun sakamakon zaben daga Gwamnati. Amma sakamakon da aka samu ya nuna dan takarar Jam’iyyar Brotherhood Mursi zai fafatawa da Shafiq a zagaye na biyu saboda rashin samun kashi 50 na kuri’un da aka kada a zagayen farko.

Wannan shi ne zaben shugaban kasa na farko da aka gudanar a kasar Masar bayan kwashe watanni ana zanga-zangar da ta yi awon gaba da gwamnatin Hosni Mubarak.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.