Mali-ECOWAS

ECOWAS/CEDEAO ta gargadi masu shiryawa gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali zagon kasa!

taron wakilan kasashen Ecowas/Cedeao
taron wakilan kasashen Ecowas/Cedeao AFP PHOTO/ SIA KAMBOU

Kungiyar gamayyar tattalin arzikin Kasashen yammacin Afrika Ecowas/Cedeao a yau tatalata a birnin Lagos na tarayyar Nijeriya, ta gabatar da kashedi bisa duk wani yinkuri da zai kawo cikas ga gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali domin ci gaba da daurewa madugun juyin mulkin ranar 22 ga watan maris gindi a kasar.

Talla

Kungiyar ta Ecowas/Cedeao ta yi nuni da dukan ranar 21 ga watan mayu da wasu masu zanga zanga suka yi wa shugaban rikon kwaryar kasar Dioncounda Traore wanda ya kai ga an kwantar da shi a asibiti.

Wakilan kasashen yammacin nahiyar Afrika guda 15, sun kara da cewa yan har yanzu siyasar kasar ta Mali dake bayan wannan al’amari na ci gaba da nausawa cikin wannan abin bakin ciki da rashin kishin kasa, domin haifar da tarnaki ga gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Mali, ta hanyar yin farfagandar ganin madugun juyin mulkin kasar Captin Amadu Sanogo ya zama shugaban rikon kwaryar kasar, wanda kuma hakan ya kaucewa tsarin sake maida kasar kan turbar amfani da kundin tsarin mulkinta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.