Najeriya

Gwamnatin Jonathan ta cika shekara a Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya cika shekara guda akan madafan iko amma an kwashe shekarar ana ruwan bama bamai tare da yaduwar cin hanci da rashawa a Najeriya, kasa mai arzikin man fetir a Afrika.

Talla

A bana ne Najeriya ke bukin cika shekaru 13 da dawo wa mulkin Demokradiya, bayan kwashe shekaru Sojoji na Mulki a kasar.

Masu sharhi akan al’amuran yau da kullum da dama, sun bayyana cewa, mulkin soji ya hana kasar ci gaba, wasu kuma ke zargin ‘Yan siyasa da dakili samun ci gaba a kasar, saboda yawan cin hanci da rashawa da ake samu, da rashin cika alkawali.

Tun kafin zaben Jonathan a shekarar 2011 bayan ya gaji gwamnatin Yar’Adua, shugaban ya yi alkawalin samar da ci gaba a Najeriya.

Goodluck Jonathan shi ne shugaba na farko da ya fito daga yankin Neja Delta.

Sai dai Masana siyasa da tattalin arziki sun ce gwamnatin Jonathan ita ce gwamnati mafi muni a Najeriya. Inda suke kira ga gwamnatin daukar matakan kawo karshen rikicin kungiyar Boko Haram.

Jonathan ya taba zama maitaimakin shugaban kasa a zamanin mulkin Ummaru Musa Yar’adua, bayan rasuwar Yar’adua ne Jonathan ya jagoranci gwamnatin rikon kwarya kafin gudanar da zabe.

A watan Mayun shekarar 2010 ne aka rantsar da Goodluck Jonathan bayan lashe zaben da aka gudanar a 2011 wanda ya haifar da tashin hankali a arewacin Najeriya.

Shekara guda da mulkin Jonathan an kai hare hare da dama a sassan yankunan arewacin Najeriya.

Hukumar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International tace sama da mutane 3000 ne suka mutu tun fara kaddamar da kai hare haren bama bamai a Najeriya

A farkon shekarar 2012 ne gwamnatin Jonathan ta bayyana janye tallafin Man Fetir al’amarin da ya haifar da zanga-zanga a sassan yankuna Najeriya saboda tsadar farashin Man fetir.

Wani Rahoto da Majalisar kasar ta fitar ya nuna Najeriya ta yi hasarar kudi Dala Biliyan 6.8 tsakanin shekarar 2009-2011 daga cikin kudaden tallafin Mai da gwamnati ke biya.

Wasu masana dai suna ganin Jonathan ba zai iya shugabancin Najeriya ba mai yawan mutane Miliyan 160 da yawan kabilu 250 wadanda yawancinsu muslumi ne da Kirista.

Amma Shugaban a lokacin da yake gabatar da jawabi domin bukin cika shekara, yace akwai ci gaba da dama da gwamnatinsa ta kawo cikin shekara guda da ya kwashe.

A kwanan baya ne Janar muhammadu Buhari madugun adawa ya yi gargadin yiyuwar ballewar rikici a Najeriya idan aka samu magudin zabe a shekarar 2015.

Janar Muhammadu Buhari shi ne ya yi hamayya da Yar’adua a zaben shekarar 2007 tare da sake karawa da Jonathan a zaben 2011 wadanda dukkaninsu ‘Yan takarar jam’iyyar PDP ne jam’iyyar da ta kwashe sama da shekaru 10 tana mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.