Sudan-Sudan ta Kudu

kasashen Sudan 2 sun koma Teburin tattaunawa a Adis Ababa

shugaban kasar Sudan Umar Hasan al-Bashir da na Sudan ta kudu  Salva Kiir
shugaban kasar Sudan Umar Hasan al-Bashir da na Sudan ta kudu Salva Kiir UN Photo/Isaac Billy

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu a yau talata ne, a birnin Adis Ababa ba kasar Ethiopia suka sake komawa wata sabuwar tattaunawar samar da zaman lafiya.

Talla

ita dai wannan tattaunawa ci gaba ne bisa wace aka  dakatar a karshen watan maris da ya gabata sakamakon barkewar yaki tare da tashe tashen hankulla babu kakkautawa a kan iyakokin kasashen 2, duk kuwa da sabon zargin ruwan wuta da kasar Sudan ta kudu ta yi a kan Sudan ta Arewa.

Tattaunawar da zata dora kan wace aka dakatar tsawon watanni 10 da suka gabata, domin magance sabanin dake tsakaninsu na kan iyaka, tun bayan samun yancin kan Sudan ta Kudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.