Masar

An kona ofishin yakin neman zaben Shafiq a Masar

Hedikwatar yakin neman zaben Ahmed Shafiq tsohon Fira minsita kuma dan takarar Shugaban kasa a Masar
Hedikwatar yakin neman zaben Ahmed Shafiq tsohon Fira minsita kuma dan takarar Shugaban kasa a Masar

Masu Zanga zanga a kasar Masar, sun kona Ofishin yakin neman zaben Ahmed Shafiq, Tsohon Fira Ministan, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa. Gidan Talabijin a kasar ya nuna masu zanga zangar na cinna wa ginin wuta, jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben a hukumance. ‘Yan Sanda sun ce sun kama mutane takwas daga cikin wadanda suka kai harin.  

Talla

Ana dai hasashen wadanda suka aikata haka masu adawa ne da Shafiq da Mursi na Jam’iyyar Brotherhood ta ‘Yan uwa musulmi. Har yanzu dai babu wani cikakken bayani game da wadanda suka kona Hedikwatar Shafiq.

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka hada wani gangami a dandalin Tahrir domin adawa da nasarar Shafiq a zaben zagaye na biyu da zai fafata da Mursi.

Faruq sultan shugaban hukumar zaben Masar yace babu wani dan takara da ya smau rinjayen kuri’u a zagaye na farko tsakanin Mursi da Shafi don sai an je ga zagaye na biyu.

Mista Sultan yace Mursi ya samu kuri'u kashi 24.77 cikin kuri’un da aka kada, Sahfiq kuma ya samu kuri’u 23.66.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.