Liberia-Saliyo-ICC

Gwamnatin Saliyo ta yaba da hukuncin dauri shekaru 50 da aka zartawara Charls Taylor

tsohon shugaban Liberia , Charles Taylor
tsohon shugaban Liberia , Charles Taylor REUTERS/Evert-Jan Daniels

Gwamnatin kasar Saliyo ta bayyana cewa gamsuwarta da hukumcin daurin shekaru 50 a gidan yari da kotun hukumta manyan laifukan cin zarafin bil’adam ta duniya ta zartar a kan tsohon shugaban kasar Laberiya Charles Taylor bisa rawar day a taka na cin zarafin Al’umma a yakin kasar ta Saliyo.  

Talla

Mataimakin ministan yada labaran kasar ta Saliyo, Sheku Tarawali, ya bayyana hukumci a matsayin wani ci gaban ga gwamnati da kuma kasar suka samu ganin cewa shara’a ta yi aikinta.

Ya kuma kara da cewa, duk da cewa hukumcin bai kai girman lafin da Taylo ya aikata ba, a zatonsa zai sanyaya zukatan mutanen da abin ya shafa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.