Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika Yayi Boni ya bukaci kafa rundunar sojan majalisar dinkin duniya kan kasar Mali
Wallafawa ranar:
A lokacin wani taron manema labarai a birnin Paris na kasar Fransa a yau laraba shugaban kasar Jamhuriyar Benin, haka kuma mai rike da shugabancin kungiyar tarayyar Afrika Thomas Boni Yayi, ya gabatar wa kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya sawarar samar da rundunar dakarun nahiyar Afrika da zasu kai dauki a kasar Mali
Shugaba Yayin Boni ya bayyana cewa, sun gabatar da wannan shawara ne domin ganin komitin samar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika, ya samu hurumin tuntubar komitin tsaro na majalisar dinkin duniya, domin ganin an hada rundunar sojan da zata kasance ta nahiyar Afrika ce, amma kuma karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, sai dai kuma ya kara da cewa, wannan matakin sojan zai biyo bayan tattaunawa ne, amma tattaunawar bazata dauki dogon lokaci ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu