Somalia

An bude taro na kwanaki biyu, na kasashe 54 kan magance rikicin kasar Somalia

rabon agajin abinci a wani sansanin yan gudun hijira na  Mogadiscio, 26 juillet 2011.
rabon agajin abinci a wani sansanin yan gudun hijira na Mogadiscio, 26 juillet 2011. AFP/ ABDURASHID ABDULLE

YAU an bude wani taro na kwanaki biyu, inda kasashe 54 ke halarta dan samo hanyar magance rikicin kasar Somalia, da kuma yadda za’a taimakawa al’ummar kasar.

Talla

Taron wanda ya samu halartar wakilan kasahse 54, da kuma bangarori dabam dabam na Yan kasar ta Somalia, zai yi nazari ne kan rikicin kasar wanda aka kwashe sama da shekaru 20 ba tare da kaukautawa ba.

Yayin da yake bude taron, mataimakin Prime Ministan Turkiya, Bekir Bozdag, yace bayan an dade ana tafka rikicin, yanzu an samu daman warware matsalar ta hanyar tattaunawa.

Taron wanda shine irin sa na biyu, wanda wanda akayi a birnin London, a watan February, ya fara da mahawara daga masana daga sassa dabam dabam kan matsalolin kasar da suka hada da samar da ruwan sha, makamashi, hanyoyi da kum atsaro.

Ana saran gobe Yan siyasa irinsu Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, shugaban kasar Somalia, Sheikh Sharif Ahmed, Prime Ministan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, da Sakataraen harkokn wajen Britaniya, William Haque zasu halarta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.