Mali-ECOWAS

Hukumomin juyin mulkin kasar Mali na binciken gano ko a kwai sojojin waje da suka shiga boren da soja suka yi

AFP/HABIBOU KOUYATE

Hukumomi a kasar Mali na bincike gameda shiga wasu sojoji cikin yunkurin kawar da Sojan dake rike da mulki, yanzu haka.

Talla

Mai gabatar da kara na Gwamnati Sombe Thera ya fadi cikin wata sanarwa cewa ana zargin sojojin da hada baki, da amfani da miyagun makamai, har ma da zargin kisa.

A ranar 30 ga wata Aprilu da kuma ranar 1 ga watan Mayu da muke ciki ne dai, wasu sojoji dake biyayya ga Gwamnatin farar hula na Amadou Toumani Toure suka nemi kawar da Sojan da suka kawar da mai gidan nasu, alamarin daya kaiga mutuwar mutane akalla 20.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.