ICC-Najeriya

Najeriya zata kafa kotun hukunta manyan laifuka a gida

Tambarin Shari'a na kotun hukunta laifukan yaki
Tambarin Shari'a na kotun hukunta laifukan yaki ICC web

Bayan yanke wa Charles Taylor hukuncin daurin shekaru 50 a gidan yari, gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin kafa kotun hukunta manyan laifuka a gida, domin gurfanar da mutanen da aka samu da laifin ta’adanci ko kashe kashe, ba tare da mika su zuwa kotun duniya ba a birnin Hague.

Talla

Najeriya ta dade da saka hannu akan dokar kotun Duniya amma sai a bana ne mahukuntan kasar suka amince Najeriya ta zama cikakkiyar Mamba.

A cewar Ministan yada labaran Najeriya Labaran Maku, matakin kafa kotun a Najeriya hanya ce ta hukunta masu laifi a gida ba tare da mika su zuwa birnin Hague ba.

Amma ‘Yan rajin kare hakkin Bil’adama sun ce wannan matakin makami ne na Siyasa domin cin zarafin wasu, musamman ‘Yan adawa ta la’akari da kalaman Goodluck Jonathan game da dokokin ta’addanci a lokacin da yake jawabi a ranar Demokradiya.

A Ranar Laraba ne kotun Hukunta manyan laifukan yaki a kasar Saliyo, ta yanke wa Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor hukuncin daurin shekaru 50 a gidan yari, bayan samun shi da laifukan yaki da suka hada da bai wa ‘Yan Tawaye makamai a Saliyo.

Hukumar kula da ‘Yancin bil’adama ta majalisar Dinkin Duniya tace hukuncin na Charles Tailor zai zama kashedi ga sauran shugabannin kasashen Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.