Malawi-Sudan-AU

An mayar da taron kasashen Afrika zuwa Addis Ababa akan takaddamar Al- Bashir

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir

An dauke taron kasashen Afrika daga Malawi zuwa birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia bayan gwamnatin Malawi ta ce ba zata karbi bakuncin shugaban kasar Sudan Umar Hassan al- Bashir. Wanda kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki ke nema ruwa a jallo.

Talla

Shugaba kwamitin masu kujerar din-din-din ne na kungiyar, Ferdinand Montcho ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai birnin Addis Ababa.

Kasar Malawi dai ta janye daga jagorantar taron ne bayan wasu bangare a cikin kasashen na Afrika sun cirje cewa sai Al- Bashir ya halarci taron wanda kasar Malawi tace bai zai yiwu ba domin kotun hukunta laifukan yaki na neman shi ruwa jallo.

Sai dai kwanakin da aka ware domin taron, daga ranar 9 ga watan Yuli zuwa ranar 16 ga watan na nan ba a canza ba.

Hukumar Diplomasiyyar kasar Sudan sun yi farin ciki da wannan mataki inda su ka ce babbar nasara ce ga diplomasiyyar kasar Sudan.

Kamfanin Dillacin Labaran Sudan (SUNA NEWS) ya rawaito cewa kokarin kotun duniya na haramtawa Al – Bashir yawo ya sha kasa.

Kamar yadda Mista Montcho ya zargi kotun Hague da tsoma baki a cikin harkokin kasashen Afirka inda ya ke cewa me ya sa a duk lokacin da kungiyar za ta yi taro sai kotun ta tsoma bakinta.

Kasar Malawi dai ta amince ne da zargin da kotun ke ma shugaba Al –Bashir na kisan kare dangi da ya faru a rikicin yankin Dafur inda sabuwar shugabar kasar , Joyce Banda ta ce ba ta bukatar Al – Bashir ya shiga kasar domin gudun fushin masu ba Malawi tallafi.

Shugaba Al Bashir, shi ne shugaban kasa na farko wanda ke kan karagar mulki da kotun ta same shi da laifin keta hakkin Bil’adama.

Mai gabatar da kara a kotun ta manyan laifuka ta duniya Luis Moreno Ocampo ya gayawa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa gazawa wajen cafke shugaba Al Bashir da mukarrabansa babban kalubale ga kwamitin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI