Masar
Shugaban Masar ya umarci majalisar kasar ta koma bakin aikin ta
Wallafawa ranar:
Shugaban Kasar Masar, Mohammed Morsi, ya baiwa rusashiyar Majalisar kasar umurnin komawa bakin aiki, har sai an gudanar da wani zabe, a wani yanayi da ake ganin zai sashi karo da Majalisar sojin kasar, wadda ta karbe aiyukan Majalisar.Wata sanarwa da jami’insa Yaseer Ali ya sanya wa hannu, tace an bukaci Yan Majalisun su cigaba da gudanar da ayyukansu, har sai an gudanar da sabon zabe, kwanaki 60 bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar.