Sudan ta Kudu

Sudan ta kudu na bukin cika shekara daya

Shugaban kudancin Sudan Salva Kiir
Shugaban kudancin Sudan Salva Kiir UN Photo/Isaac Billy

Yau kasar Sudan ta kudu, ke bikin cika shekara guda da kafuwa, sai dai tashin hankali da talauci sun hana kasar cigaba, ganin irin fadi tashin da aka samu a cikin shekarar da ta gabata.Duk da cigaban da ake cewa an samu, Sudan ta kudu, na cikin kasahsen da suka fi talauci a duniya, duk da arzikin man da take da shi, abin da ya sa mataimakin shugaban kasar, Rick Machar, yace sun gaza wajen cimma biyan bukatar al’ummar kasar.Kasashen duniya na ta aikewa da sakon taya murna ga al’ummar kasar.