Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Nijeriya ya ce Afrika na fuskantar sabbin matsaloli

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya bayyana sabbin matsalolin dake addabar nahiyar Afrika, a matsayin wani babban kalubalen dake mayar da nahiyar baya. Yayin da yake bude taron matan shugabanin Afrika, shugaba Jonathan ya kara da cewa.yayin da kasashen nahiyar ke kokarin magance tsoffin laifufuka, wasu sabbi irin su fataucin miyagun kwayoyi da safarar mata, sauyin yanayi, satar jama’a, garkuwa da mutane, talauci, fadan kabilanci da na addini sun mamaye kasashen nahiyar, yayin da a ko da yaushe aka samu haka, mata kan fada cikin halin kaka-ni-kayi. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.