Masar

Shugaban Masar ya kori Tantawi

Sabon Shugaban kasar Masar Mohamed Morsi.
Sabon Shugaban kasar Masar Mohamed Morsi. Reuters

Shugaban Masar, Muhammad Mursi, ya kori ministan tsaron kasar mai karfin fada a ji, Field Marshal Hussein Tantawi daga mukamin Ministan tsaro tare da Soke sauye sauyen da Sojoji suka yi wa kundin tsarin Mulki da suka takaita ikon shugaban kasa.

Talla

Kakakin shugaban kasar, Yasir Ali, shi ne ya bayar da sanarwar ta gidan talabijin. Matakin da ya sa magoya bayan shugaban suka shiga murna a dandalin Tahrir a birnin al Kahira.

Tantawi ya taba zama shugaban rikon kwarya bayan kawar da Hosni Mubarak na fiye da shekara guda. bayan hawan Mursi shugaban kasa aka ba shi mukamin Ministan tsaro a kasar.

Sanarwar tube Tantawi ya nuna adawar da ke tsakanin Gwamnatin Mursi da Sojin Masar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.