Najeriya

An samu malalar mai kusa da kamfanin Exxon Mobile a Najeriya

Kamfanin Mai na Exxon Mobile
Kamfanin Mai na Exxon Mobile (Photo : Reuters)

An samu malalar mai, a yankunan bakin teku a kudancin Najeriya inda kamfanin man Exxon Mobile na kasar Amurka ke gudanar da ayyukan shi. Kamfanin ya tabbatar da samun malalar a gabar tekun Akwa Ibom da ke kudancin kasar, a daidai lokacin da mazauna yankin ke cewa sun gani da idonsu Mai yana malala.

Talla

Sai dai kamfanin na ExxonMobil yace har yanzu bai gano dalilin yawan malalar ba.

Irin wannan malalar tana yawan faruwa a yankin Neja Delta, saboda dalilan da suka hada da, kafar ungulu da barayin mai ke yi, da kuma rashin kula da kayan aiki daga bangaren kamfanonin mai, da ke aiki a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.