Najeriya

Bom ya kashe Mutane uku a Kaduna

Mutane kimanin uku ne suka rasa rayukansu a garin Kaduna da ke Arewacin Niajeriya, sakamakon fashewar bom a lokacin da wasu mutane biyu ke dauke da shi a kan babur saman hanyar zuwa Masallacin Juma’a na Sultan Bello.

Gawawwakin wadanda suka mutu saman babur  sakamakon fashewar Bom a Kaduna Tarayyar Najeriya
Gawawwakin wadanda suka mutu saman babur sakamakon fashewar Bom a Kaduna Tarayyar Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Kakakin ‘Yan Sandan Jahar Abubakar Balteh yace da misalin karfe 3:50 na yamma Agogon Najeriya ne wasu mutane biyu saman babur suka mutu sakamakon fashewar wani abu da ake zaton Bom ne akan Titin Ali Akilu.

Ana zaton sun yi kokarin kai wa Sheikh Ahmad Gumi hari ne saboda yadda malamin ke wa'azin adawa da lamurran kungiyar Boko Haram.

Jami’in kungiyar Agaji ta Red Cross Shehu Umar Abdul yace wasu mutane biyu sun mutu wadanda ke tafiya kusa da inda al’amarin ya auku.

Babu dai wani tabbaci game da inda maharan suka nufa domin kai harin bom din.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI