Najeriya

Dubban mutane suna gudun hijira a Damaturu

Jami'an tsaro tare da mutane Damaturu a gaban gawawwakin mutane da suka mutu sanadiyar harin Bom
Jami'an tsaro tare da mutane Damaturu a gaban gawawwakin mutane da suka mutu sanadiyar harin Bom Leadership Newspaper

Daruruwan mazauna Damaturu ne a Arewacin Najeriya ke gudun hijara daga birnin bayan zargin Jami’an tsaro suna bi gida-gida suna cafke mutane da suke zargin ‘Yan Boko Haram ne da kuma jita-jitar da ake yi game da sabbin hare haren da kungiyar Boko Haram za ta kaddamar.

Talla

A ranar Lahadi an samu mutuwar mutane biyu bayan wata musayar wuta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da wasu da ake zargin ‘Yan Boko Haram ne inda Jami’an tsaron suka ce sun kashe ‘Ya’yan kungiyar sama da 30.

Dubban mazauna garin Damaturu ne suka cika tasoshin shiga mota domin kauracewa garin.

Rahotanni sun ce a unguwar Pindigari yankin ya koma kamar an yi ruwa an dauke bayan musayar wuta da aka yi tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan Boko Haram.

Akwai jita jitar cewa kungiyar Boko Haram za ta kaddamar da sabbin hare hare bayan kammala Azumin Ramadan lokacin Salla. Amma Jami’an tsaro sun karyata jita jitar.

Shugaban rundunar ‘Yan sandan Jahar Yobe Patrick Egbuniwe, yace Kungiyar Boko Haram ce ke yayata jita jitar domin rikita mazauna garin su gudu.

Garin Damaturu ya dade yana fama da hare haren bama bamai da ake alakanta su da Kungiyar Boko Haram.

Sai dai ana zargin Jami’an tsaro da cin zarafin mutane tare da keta hakkinsu da sunan farautar ‘Yan Kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI