Amfani da karfin Soji a Mali ya zama dole-Jonathan
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace ya zama dole dakarun kasashen Afrika su shiga tsakanin rikicin kasar Mali a yankin Arewaci idan aka kasa cim ma yarjejeniya da mayakan Ansar Dine da suka karbe ikon yankin.
Jonathan wanda ke ziyarar kwanaki biyu a kasar Senegal yace hanyar Diflomasiya ko sasantawa ita ce hanya ta farko amma daukar matakin Soji shi ne mataki na karshe idan matakin sasantawa ya cutura.
Bayan ganawa da Macky Sall shugaban kasar Senegal, Shugaban Najeriya yace sai kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta nemi izinin Majalisar Dinkin Duniya kafin daukar matakin Soji a kasar Mali.
A makon nan ne aka kafa sabuwar gwamnatin hadin kai karkashin jagorancin ECOWAS domin kokarin magance rikicin kasar Mali.
Sojoji ne suka kafa gwamnatin rikon kwarya bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Amadou Toumani Toure a ranar 22 ga watan Maris.
A lokacin juyin mulkin ne ‘Yan Tawayen kasar tare da mayakan Ansar Dine suka samu nasarar karbe ikon yankin Arewaci yankin da girmansa ya fi kasar Faransa girma.
Sai dai Goodluck Jonathan ya yi watsi da daukar matakin Soji domin karya ‘Yan Kungiyar Boko Haram a kasar shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu