Najeriya

Gwamnoni Arewacin Najeriya sun kafa kwamitin magance matsalar tsaro

Gwamnan Jahar Niger Babangida Aliyu
Gwamnan Jahar Niger Babangida Aliyu

Gwamnonin Jahohin Arewacin Najeriya da ke fama da tashin bama bamai sun nada wani kwamitin mutane 41 wanda zai diba hanyoyin magance matsalar tsaro da ta addabi yankin tare da zama teburin sasantawa da wadanda al’amarin ya shafa.Sanarwar nada kwamitin bai bayyana sunan wata kungiya ba ko kungiyar Boko Haram da ake zargin sun kashe mutane sama da 1,400 a sassan arewacin Najeriya.

Talla

Gwamnonin sun ce kwamitin mai cin gashin kansa ne wanda zai taimaka domin warware matsalolin da suka shiga.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI