An yi jana’izar tsohon Firaministan Habasha, Meles Zenawi
Dubbanin ‘Yan kasar Habasha da akalla shugabanin kasashe 15 su ka halarci birnin Addis Ababa, domin yin bankwana da gawar tsohon Firaministan kasar Ethiopia, Meles Zenawi, wanda ya rasu a watan jiya aka kuma yi jana’izarsa a jiya Lahadi.
Wallafawa ranar:
An dai lullube akwatin daukan gawar tsohon shugaban kasar na Habasha ne da kyalle mai launin tutar kasar wacce da launin kore, ja da kuma ratsin ruwan kwai a tsakiya.
Inda kuma aka daura shi akan wani abun tafiya baki wanda ke tafiya a hankali a cikin jerin gwano daga gidansa zuwa babban filin da ake kira Meskel Square.
Cikin jerin gwanan daga gidan nasa, akwai manyan hafsoshin soji da kuma Malaman addinin kasar.
An kuma ajiye akwatin daukan gawar Zenawi ne a gaban dubbanin mutanen da su ka taru a filin na Meskes Square domin bankwana da tsohon shugaban nasu.
Wasu daga cikin mutanen na ta kada tutar kasar, a yayin da wasu kuma ke ta tafka kuka a lokacin da sabon Firaministan kasar da sauran shugabanin kasashen Afrika ke gabatar da bayanan ban kwana.
Jirage masu saukar angulu dauke kuma da launin azurfa sun yi ta shawagi domin girmama marigayin.
Haka kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya ya barke a dai dai lokacin aka doshi babbar majami’ar Holy Trinity Cathederal, inda aka a gudanar da addu’oin binne Meles Zenawi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu