An fara sako mahaka ma’adinan Afrika ta Kudu
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wata kotun kasar Afrika ta Kudu za ta fara sako mahaka ma’adinan kasar su 270 bayan kisan da ‘Yan sanda su ka yiwa wasu daga cikin abokan aikinsu wanda ake zraginsu da tunzura kisan.
Bayan wani bore da ‘Yan kasar ta Afrika ta Kudu su ka yi ne, Shugabar shigar da kara a kasar, Nomgcobo Jiba, ta ce za ta sake duba laifukan da ake zargin mahaka ma’adinan da su.
“Laifukan kisan da ake zargin ma’aikat su 270, za a janye karar a zaman kotun da za a yi nan gaba”, inji Jiba, a hirar ta da Kamfanin Dillancin labaran AFP.
A cewar ta, a yau Litinin ne za a fara sako mahaka ma’adinan.
Ta ce tuni an riga har an tabbatar da lambobin gidan 140 daga cikin ma’aikatan inda ta kara da cewa sauran kuma nan da zuwa Alhamis duk za su tafi gida.
Ana dai tuhumar mahaka ma’adinan da laifin kisan abokanan aikinsu 34 da ‘Yan sanda su ka kashe, wanda aka daura laifin a kansu bayan zarginsu da aka yi da tunzura ‘Yan sandan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu