Afrika ta Kudu

Mahaka ma’adinan Afrika ta Kudu sun yi jerin gwano

Daruruwan mahaka ma’adinai a kasar Afrika ta Kudu wanda ke yajin aiki sun yi wani jerin gwano a yankin Lonmin Marikana domin nuna bakin cikinsu akan kashe mutanen da aka kashe da kuma batun karin kudade.

Wasu daga cikin ma'aikatan mahakar Lonmin a lokacin da su ka yi jerin gwano
Wasu daga cikin ma'aikatan mahakar Lonmin a lokacin da su ka yi jerin gwano REUTERS/Mike Hutchings
Talla

An ga jiraga masu saukar angula suna shawagi a yankin a yayin da mahakan, dauke da sanduna suna waka suna kuma dosar yankin da abin ya faru.

A jiya dai kotu a kasar ta fara sako wasu daga cikin ma’aikatan domin zarginsu da ake yi na kashe abokanan aikinsu.

Gwamnatin kasar ta yi kokarin shiga tsakani domin kawo karshen rikicin da kuma yajin aikin wadanda su ka gurgunta ayyuka a mahakar ta Lonmin.

An ji wasu daga cikin ma’aikatn na ikrarin cewa, sun fito ko a sasanta game da maganar karin kudin ko kuma duk abin da zai faru ya faru.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI