Sabon shugaban bankin duniya, Kim ya fara ziyararsa da nahiyar Afrika
Sabon shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim, ya fara ziyararsa da nahiyar Afrika inda ya fara yada zango a kasar Cote d’Ivoir domin tattauna yadda za a habaka harkokin kasuwanci a yankin.Kim ya karbi shugabancin bankin na duniya ne a farkon watan Yunin bana, a ziyara tasa ya kuma gana da shugaban kasar Alassane Ouattara, inda daga baya su ka yi wata liyafa.
Wallafawa ranar:
Shugaban bankin na duniya kuma, ya fara da kasar ne domin tattaunawa akan muhimmancin zaman lafiya.
“Ga alama ina ganin cewa yanzu akwai zaman lafiya, za kuma a sami cigaba ta fannin kasuwanci ne, idan akwai zaman lafiya”, inji Kim
Ya kuma kara da cewa, idan kuma har kasa na so ta samu cigaba mai dorewa, dole ne a saka mata a cikin harkokin kasuwanci, musamman matasa.
Ouattara ana shi bangaren, ya yi farin ciki da Kim ya fara ziyararsa da nahiyar ta Afrika, a sabon aikin nasa.
Ya kuma kara da nuna kyakyawan zaton cewa bankin na duniya zai nuna sassauci ta inda kasar ta Cote d’Ivoir da nahiyar ta Afrika za su cigaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu