Mali

Gwamnatin kasar mali ta nemi taimakon dakaru daga kungiyar Cedeao

Gwamnatin kasar Mali ta bukacin kungiyar bunkassa tatalin arzikin afrika ta yaman CDEAO da ta kawo mata gudunmuwar na gani cewa, an kawo karshen masu maida zaune tsayen a yankin arewacin kasar.Inda a yanzu haka wata tawaga ke kan hanyar zuwa Babban Birni Abidjan na kasar Cote D’Ivoire domin tautaunawa da Alassane Watarra kan wannan Al’amari.Ajiya talata ne, Shugaban gwamnatin Rikon kwaryar kasar Mai Dionkounda taraoare ya bukaci taimakon dakarun kasashen Afrika ta Yamma domin sake kauto yankin arewacin kasar da masu kishin Islama suka mamaye.Tuni dai, Kungiyar CEDEA ta ce, a shirye take ta aika da dakaru 3.300 a yakin arewacin na Mali amma ta tsaya tana jiran amincewar MDD. 

shugaban kasar Cote d'Ivoir, shugaban kungiyar Cédéao, Alassane Ouattaranne a ranar  5 septembre à birnin Abidjan na ganawa da Baba Berthe sakataren fadar shugaban kasar  Mali, da kuma Amadou Ousmane Touré jakadan Mali a Côte d'Ivoire.
shugaban kasar Cote d'Ivoir, shugaban kungiyar Cédéao, Alassane Ouattaranne a ranar 5 septembre à birnin Abidjan na ganawa da Baba Berthe sakataren fadar shugaban kasar Mali, da kuma Amadou Ousmane Touré jakadan Mali a Côte d'Ivoire. AFP/Sia Kambou