Maroko

kungiyoyin kare hakkin dan adam a Maroko sun yi tir da korar bakin da Gwamnatin kasar ke yi.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar Morocco sun la’anci Koran baki ba kan gado da Hukumomin kasar suka fara farkon wannan mako.Kungiyoyin na yin Allah wadai ne da yadda jami’an tsaro da kartin wufi kan rika lakadawa baki dukan tsiya kafin ayi masu Koran wulakanci daga kasar.Kungiyoyin sun ci gaba da cewa, yanzu haka akwai bakin haure kusan dubu 25 a kasar.