Ghana

Shugaban Ghana, Mahama ya kaiwa Ouattara ziyara

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahamma, da takwaransa na Cote d’I voire, Alassane Outtara, sun gudanar da tattaunawa ta musamman kan batutuwan da suka shafi tsaro akan iyakokin kasashen biyu.Sun gudanar da tataunawar ce a lokacin ziyarar da shi John Dramani ya kaiwa shugaban kasar Cote d’Ivoire, Alassane Outtara, a karon farko tun bayan zarginda Outtara ya yiwa magoya bayan Laurent Gbangbo na alhakin kai hare- hare.  

Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama
Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama Wikipedia
Talla

Ouattara dai na zargin masu kai hare-hare da akan kaiwa Soji da ‘yan sandansa, akan ‘Yan tawaye kasar Cote d’Ivoire da su ka tsere kasar Ghana.

Shugaban kasar Ghana ya bayyana cewar ba za’a taba amfani da yankin Ghana wajen kai hare hare, domin tabarbarar da zaman lafiya a kasar Cote d’Ivoire ba.

Ya ce sun riki zaman lafiyar kasar Cote d’Ivoire da muhimmanci kamar na kasarsu ta Ghana.

Mahama ya ce fatansu shi ne suga kasar Cote d’Ivoire cikin walwala da cigaba kamar dai yanda suke ta fata ga kasar tasu.

Ziyarar dai wani rangadi ce ta godiya da shugaban kasar ke kaiwa ga shugabannin Nahiyar Afrika da suka halarci Jana’izar tsohon shugaban kasar daya rasu a kwanan baya wato John Ata Mills.

Shugaban kasar Ghana ya kuma bayyana karara cewar daga yanzu zasu rika bada mafaka ga duk wani dan Ivory Coast dake bukata, saboda faruwar wani abu mai hatsari ga rayuwarsa a kasarsa, bisa tanadin doka.

Amma ya ce ba zasu bari ayi amfani da kasar ba domin aikata katobarar da zata zubar da mutuncin kasar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI