Chadi

Shugaban ‘Yan tawayen Chadi, Baba Ladde ya mika kansa

Taswirar kasar Chadi
Taswirar kasar Chadi © RFI

Shugaban ‘Yan tawayen kasar Chadi na kabilar Fula, AbdelKader Baba Ladde, da dakarun kasar ke nema ruwa a jallo, ya koma birnin Ndjamena ya kuma mika kansa ga dakarun kasar Afrika ta tsakiya.

Talla

Rahotanni daga Chadin sun ce Ministan tsaron kasar Chadin ne ya tarbi shugaban ‘Yan tawayen bayan saukarsa filin saukar jirgin sama a Ndjamena.
Mista Ladde ya ce ya dawo ne domin samar da zaman lafiya a kasar Chadi tare da kira ga sauran ‘Yan tawayen su bi sahun shi.
 

“Na yi murna da dawowa gida, ina kuma fatan sauran za su bi sahu, ba wai FPR ta dawo ne dan ta nema wasu biyan bukatunta bane, bamu da wata bukata, burin mu shi ne a samu zaman lafiya a kasarmu da kuma yankin baki daya”, inji Baba Ladde.

Babba Ladde dai ya kasance da yana fafutukar neman wa ‘Yan kabilarsa ‘yanci, wadanda ke zaune a kasashe daban daban a nahiyar Afrika.

Amma a ranar Lahadi ya mika kansa a kasar Afrika ta tsakiya bayan wata tattaunawa da aka yi da Majalisar Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI