Hassan Sheikh Mohamud ne sabon shugaban kasar Somalia
‘Yan Majalisar Dokokin kasar Somalia a sun zabi, Hassan Sheikh Mohamud, a matsayin sabon shugaban kasar Somalia bayan ya sami mafi rinjayan kuri’u a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar. Sheikh Mohamud ya kara ne da tsohon shugaban kasar Sharif Sheikh Ahmed.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sheikh Mohamud, dan shekaru 59, ya samu kuri’u 190, a yayin da tsohon shugaban kasar Sheikh Ahmed ya samu kuri’u 79.
Da farko da ‘Yan takaran su biyu na tafiya da kunnen doki ne amma Sheikh Mohamud sai ya lashe zaben a zagaye na biyu.
“Hassan Sheikh Mohamud ne ya lashe zaben shugaban kasan da aka gudanar a yau,” inji Kakakin Majalisar Dokokin, Mohammed Osman Jawari, a lokacin da ya ke sanar da sakamakon zaben.
Wasu ‘Yan takara biyu, wadanda su ka hada da Firaminita mai baring gado, Abdiweli Mohammed Ali, da Abdikadir Osoble, sun fice daga cikin takarar a zagaye na farko, a cikin zaben wanda Majlisar dinkin Duniya ta marawa matakan gudanar da shi baya, don ganin cewa an samar da sabuwar gwamnatin a kasar wacce ke fama da rikici.
Hassan Sheikh Mohamud ba wani sanannen dan takara ba ne, ya kuma zo ne daga cikin ‘Yan kabilar Hawiye.
Masu fashin bakin akan harkokin siyaysa sun ce ya dade yana aiki tare da kungiyoyi masu zaman kansu a kasar ta Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu