Somalia

‘Yan majalisa za su zabi sabon shugaban kasa a Somalia

Majalisar Kasar Somalia, za ta zabi sabon shugaban kasa, tsakanin ‘Yan takara 25 a wani mataki na kawo karshen yaki a kasar da aka kwashe shekaru ana yi. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana zaben a matsayin mai dimbin tarihi.

'Yan Majalisar somalia suna Sallah bayan rantsar da su
'Yan Majalisar somalia suna Sallah bayan rantsar da su REUTERS/Stuart Price/AU-UN IST PHOTO/Handout
Talla

Kasar Somalia na ci gaba da fama da tashe tashen hankula, tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Siad Barre, abinda ya sa aka kasa samun tsayayyiyar gwamnatin da ta samu karbuwa a kasar.

Kuma har yanzu kungiyar Al shabeb ce ke rike da ikon wasu yankunan kudancin kasar, inda kungiyar ta dade tana kai hare haren kunar bakin wake a Mogadishu kafin su fice daga babban birnin kasar.

Shugaba mai ci Sheikh Sharif Sheikh Ahmed wanda ke jagorantar kasar tun a 2009, shi ne ake sa ran zai lashe zaben tsakanin ‘Yan takara 24 wadanda kuma ke zarginsa da cin hanci.

Babban mai hamayya da shugaban shi ne Firaminista Abdiweli Muhammed Ali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI