Kenya

An kafa dokar hana fita a yankin Tana kasar Kenya

Shugaban Kasar Kenya, Mwai Kibaki, ya kafa dokar hana fita a yankin Tana, inda mutane 38 suka rasa rayukansu, sakamakon rikicin kabilanci. Shugaban ya kuma bukaci jami’an tsaro da su dauki tsauraran matakai kan masu kitsa tashin hankalin, wanda ya lakume rayukan mata da kananan yara da jami’an tsaro.

Dakarun Kenya suna sintiri a Yankin Tana kasar Kenya
Dakarun Kenya suna sintiri a Yankin Tana kasar Kenya
Talla

Rahotanni sun ce, wasu ‘Yan bindiga ne suka yi kawanya ga wasu kauyuka, inda suka cinna musu wuta, tare da kuma abka wa mutanen da ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI