Afrika ta Kudu

Malema ya yi kiran shiga yajin aiki a Afrika ta Kudu

Julius Malema Shugaban Matasan Jam'iyyar ANC mai murabus a Afrika ta Kudu
Julius Malema Shugaban Matasan Jam'iyyar ANC mai murabus a Afrika ta Kudu Reuters

Shugaban matasan Jam’iyar ANC, Julius Malema, mai murabus ya yi kiran yajin aikin gama gari, dan ganin an biya wa ma’aikatan ma’adinai bukatunsu, matakin da ake ganin zai jefa kasar cikin tashin hankali.

Talla

Yayin da ya ke jawabi ga taron ma’aikatan da ke zanga zanga a jiya Talata, Malema yace ya zama wajibi mutanen da ke sadaukar da rayukansu wajen hako ma’adinan su amfana da arzikin da ake tonowa, wajen kara musu albashi dai dai da aikin da suke yi.

Wanan zanga zanga a baya, ta yi sanadiyar mutuwar mutane 44.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.