Najeria

Najeriya ta ciyo bashin kudi Dalar Amurka 600 daga Sin

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zantawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zantawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa. REUTERS/Afolabi Sotunde

Hukumomin Najeriya sun ciwo bashin Dala miluyan 600 daga bankin Sin, domin gina hanyoyin jiragen kasa. Rahotanni sun ce bashin wanda za’a dinga biyan ruwan kashi biyu da rabi, za’a biya shi ne a cikin shekaru 20 masu zuwa. 

Talla

Kamfanin Dillancin labaran Reuters, ya ruwaito cewar, kudin kwangilar wanda kamfanin Sin ke yi, ya kai Dala miliyan 500, yayin da za’a kashe miliyan 100 wajen aikin samar da tsaro.

Kasar Sin dai tabawa wasu kasashen Afrika basussuka mai rahusa a ‘yan shekarun da su ka gabata.

Gwamnatin ta Najeriya na sa ran saka hanu a wata yarjejeniya a makwanni masu zuwa inda za ta kara karban bashin kudi na Dalar Amurka 500 domin gina filayen saukar jirage hudu a babban birnin kasar Abuja, da Jihar Kano da garin Port Harcourt da Jihar Enugu, kamar yadda Ma’aikatar samar da kudade ta fada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI