An cafke mutane da dama a Libya bayan kai hari Ofishin jekadancin Amurka
Wallafawa ranar:
Mahukuntan kasar Libya sun cafke mutane da dama da ake zargin suna da hannu wajen kai hari a ofishin jekadancin Amurka wanda ya yi sanadiyar mutuwar Jekadan Amurka a Benghazi a ranar Talata domin nuna fushin su ga wani Fim da ya ci zarafin Manzon Allah.
A yau Juma’a akwai yiyuwar ballewar Zanga-zanga a kasashen Musulmi bayan kammala Sallar Juma’a.
A kasar Masar ‘Yan Sanda da Masu zanga-zanga sun yi arangama da juna a birnin Al Kahira inda kuma a yau Jumu’a Jam’iyyar Musulmi ta Brotherhood ta yi kiran gudanar da zanga-zangar lumana.
Firaminsitan Libya Mustafa Abu Shaqur yace suna ci gaba da bincike domin gano wadanda suka kai hari a ofishin jekadancin Amurka.
Shugaban Amurka kuma Barack Obama ya sha alwashin kare rayukan Amurkawa a kasashen Waje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu