Malaman Addini sun yi kiran gudanar da Zanga-zanga a Sudan
Manyan Malaman Addini a kasar Sudan sun yi kiran gudanar da zanga-zangar adawa da Fim wanda ke nuna cin zarafin Manzon Allah da aka samar daga kasar Amurka, tare da gargadin kai wa Ofishin jekadancin Amurka hari.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun bayan fitar da Fim din ne zanga-zanga ta barke a kasashen Musulmi inda masu zanga-zangar suka shiga kona ofishin jekadancin Amurka tare da yaga tutar kasar a kasashensu.
Ministan harakokin wajen Sudan ya soki gwamnatin Jamus saboda rashin daukar matakain haramta zanga-zanga da wasu suka yi dauke da wani hoto da suka alakanta shi da Manzon Allah SAW, inda kuma Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayar da lambar yabo ga wani dan kasar Denmark da ya ci zarafin Manzon Allah.
Majalisar Malamai wadanda ke Magana da yawun gwamnati sun ce akwai Masallatai sama da Dubu Dari Biyar a Khartoum don haka za su yi kira ga Al’ummar Musulmi a hudubar Juma’a domin fitowa zanga-zangar kare Manzon Allah.
Tun a ranar Laraba ne wasu suka kaddamar da zanga-zanga a harabar ofishin jekadancin Amurka a Khartoum.
Manyan jekadun Amurka guda hudu ne aka kashe da suka hada da jekandan Amurka a Benghazi bayan fitar da Fim din a intanet.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu