Nijar

Mutane 162 suka mutu a Nijar, inji MDD

Ambaliyar Ruwa a birnin Agadez
Ambaliyar Ruwa a birnin Agadez

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane 81 suka mutu sakamakon ambaliyar Ruwa da ta shafi Jamhuriyar Nijar tun a watan Yuni tare da bayyana cewa cutar amai da gudanawa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 81.

Talla

Alkalumman da da Jamhuriyyar Nijar ta fitar a baya sun nuna mutane 68 ne suka mutu tare da bayyana cewa mutane 485,000 ambaliyar ruwan ta shafa.

Ambaliyar ta ci gidaje da makarantu da masallatai da dama tare haifar da hasarar dinbim abinci a kasar.

Bayan samun ambaliyar Ruwan, Majalisar Dinkin Duniya tace an samu barkewar Amai da gudawa a yankin Tillaberi da ke kan iyaka da Mali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.