Faransa

An Bude Sabon Dakin Ajiyan Kayan Tarihi A Faransa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya la'anci fasalin tabarbarewar tsaro a kasar Mali, da yadda ‘yan tawaye ke tarwatsa wuraren adana kayan  tarihi dake kasar.Shugaban Faransa  na magana ne  a lokacin da yake kaddamar da wurin adana  kayan tarihi a garin Lourve na kasar Faransa.Wannan wurin adana kayan tarihi da suka shafi addinin musulunci, ya kasance na farko babban wajen ajiyan kayan tarihi a fadin duniya.An gina sabon wajen ajiyan kayan tarihin a kan kudin Turai, Euro miliyan 100 kuma Gwamnatin kasar Faransa ta dauki nauyin ginashi.Tsohon Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy ya aza harsashin ginin a shekara ta 2008. 

SShugaban kasar Faransa Francois Hollande yana duba kayan tarihi a sabon wurin dake Louvre
SShugaban kasar Faransa Francois Hollande yana duba kayan tarihi a sabon wurin dake Louvre RFi/Reuters