Ghana-Cote D'ivoire

Ghana Ta Kama 'Yan Kasar Cote D'ivoire

‘Yan Sanda a kasar Ghana na tsare da wasu mutane uku ‘yan kasar Cote D’Ivoire da aka kama suna cinikin makamai da niyyar kaiwa kasar su domin kifar da Gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara.Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda na kasar Ghana, Stephen Andoh-Kofie ne ya sanar da wannan kame.Ya bayyana cewa shigan burtu jami'an tsaron kasar Ghana suka yi, suka tinkari masu bukatar sayen makaman a matsayin suna da irin makaman da ake bukata. 

Shugaban kasar Cote d'Ivoire  Alassane Ouatara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouatara RFi/Reuters